12 Satumba 2020 - 13:07
​Sylva: Najeriya Za Ta Samu Rarar Sama Da Naira Tiriliyan 1 Sakamakon Cire Tallafin Mai

Karamin ministan albarkatun mai a Najeriya Timipre Sylva, ya bayyana cewa, Najeriya za ta samu rarar sama da naira tiriliyan daya a kowace shekara, sakamakon cire tallafin mai da aka yi.

ABNA24 : Ministan ya bayyana cewa, an samu nasarar tanadar naira biliyan 500 daga wadannan kudade wajen aiwatar da kasafin kudin shekarar 2020.

Ya kara da cewa, bisa yadda aka gyara bangaren mai, hakan zai saukaka wa masu zuba jari wajen samun damar zuba kudadensu a matatun mai na Najeriya, saboda haka cire tallafin mai da gwamnati ke bayarwa yin hakan babban alhairi ga dukkanin ‘yan Najeriya.

Ya ci gaba da cewa, idan aka samu ‘yan kasuwa daga ciki da waje suka zuba hannayen jari a bangaren harkokin mai na Najeriya, hakan zai taimaka wajen samar da ayyukan yi ga jama’a, kuma kasa za ta kara samun kudaden shiga, wanda hakan zai taimaka ma talakawan kasar.

Da dama daga cikin mutanen Najeriya dai suna yin korafi a kan cire tallafin man da gwamnati ta yi, wanda hakan yasa a halin yanzu farashin kowace lita guda ya haura Naira 160, wanda kuma ake ganin cewa hakan zai yi tasiri a kan farashin sauran dukkanin kayan masarufi a kasar.

342/